Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, murnar cika shekara 83 da haihuwa.
A wata sanarwa daga fadar shugaban kasa ta fitar, Tinubu ya bayyana Abdulsalami a matsayin gwarzo, mai gaskiya da rikon amana, wanda ya taka rawar gani wajen wanzar da zaman lafiya da cigaban dimokuradiyyar Najeriya.
Shugaban ya jaddada muhimmiyar rawar da Abdulsalami ya taka wajen mika mulki cikin kwanciyar hankali a shekarar 1999, wanda ya haifar da Jamhuriyya ta Hudu.
Ya kuma yaba da kokarin da Janar Abdulsalami ke ci gaba da yi a matsayin shugaban Kwamitin Zaman Lafiya na Ƙasa, musamman wajen ƙarfafa fahimtar juna, rage rikice-rikice, da tabbatar da zaman lafiya a lokacin zabe da bayan zabe.
