Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuTarihi ba zai manta da gudunmawarka ga dimukraɗiyyar Nijeriya ba - Sakon...

Tarihi ba zai manta da gudunmawarka ga dimukraɗiyyar Nijeriya ba – Sakon Tinubu na taya Abdulsalami murnar cika shekara 83 da haihuwa

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, murnar cika shekara 83 da haihuwa.

A wata sanarwa daga fadar shugaban kasa ta fitar, Tinubu ya bayyana Abdulsalami a matsayin gwarzo, mai gaskiya da rikon amana, wanda ya taka rawar gani wajen wanzar da zaman lafiya da cigaban dimokuradiyyar Najeriya.

Shugaban ya jaddada muhimmiyar rawar da Abdulsalami ya taka wajen mika mulki cikin kwanciyar hankali a shekarar 1999, wanda ya haifar da Jamhuriyya ta Hudu.

Ya kuma yaba da kokarin da Janar Abdulsalami ke ci gaba da yi a matsayin shugaban Kwamitin Zaman Lafiya na Ƙasa, musamman wajen ƙarfafa fahimtar juna, rage rikice-rikice, da tabbatar da zaman lafiya a lokacin zabe da bayan zabe.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata