Tsohon gwamnan Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kasancewa cikin masu goyon bayan soke zaben 12 ga Yuni, 1993, wanda marigayi MKO Abiola ya ci.
A wata hira da Arise TV, Lamido ya ce mahaifiyar Tinubu, Hajiya Abibatu Mogaji, ta jagoranci mata ‘yan kasuwa daga Legas zuwa Abuja domin marawa IBB baya bayan soke zaben.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Lamido na cewa Tinubu bai bayyana a siyasa ba sai bayan mulkin Abacha, inda ya samu mukami a majalisar dattawa. Ya ce Tinubu yana ƙoƙarin kirkirar tarihin siyasa da bai da shi, yana nuna kansa a matsayin gwarzon demokuradiyya.
A cewar Lamido, ƙungiyar NADECO da ake danganta wa da fafutukar dawo da demokuradiyya ba wai domin kare nasarar Abiola aka kafa ta ba, sai dai don kalubalantar mulkin Abacha.
