Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuTinubu na iya sauya Shettima da Kirista daga Arewa ta Tsakiya ...

Tinubu na iya sauya Shettima da Kirista daga Arewa ta Tsakiya – Dr. Sam Amadi

Dr. Sam Amadi ya yi hasashen cewa Shugaba Tinubu na iya sauya Shettima da Kirista daga Arewa ta Tsakiya, a wani yunkuri na sassauta tasirin tsarin Musulmi-Musulmi da karfafa yankin da bai taba samun shugabanci ba tun 1999.

Jaridar Punch ta ruwaito masanin siyasar na cewa, alamu sun nuna sauyin yanayi a siyasar APC, inda Tinubu ke da tarihin sauya mataimaka tun lokacin da ya ke gwamnan Legas.

Hasashen na Amadi ya zo ne a daidai lokacin da ake rade-radin sabani tsakanin Tinubu da Shettima, musamman bayan an gaza ambato sunan Shettima a taron jam’iyyar APC da aka gudanar a Gombe lamarin da ya tada kura a kafafen siyasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata