Tuesday, April 7, 2026
HomeBabban LabarinmuTinubu ya samu lambar yabo mafi girma ta ƙasar Saint Lucia

Tinubu ya samu lambar yabo mafi girma ta ƙasar Saint Lucia

Gwamnatin ƙasar Saint Lucia ta karrama Shugaba Bola Ahmed Tinubu da lambar yabo mafi girma ta ƙasar—Knight Commander of the Order of Saint Lucia (KCOSL)

Sanarwar hakan ta fito ne daga shafin X na ofishin Firayim Ministan ƙasar, inda aka bayyana cewa Gwamna Janar na Saint Lucia ya amince da ba Tinubu wannan kambin, bisa shawarar gwamnatin kasar.

Rahoton jaridar The Nation ya bayyana cewa an yi wannan karrama ne saboda jagorancinsa na ƙwarai a nahiyar Afirka, da jajircewarsa wajen haɓaka haɗin gwiwar ƙasashe masu tasowa, da kuma ƙoƙarinsa na farfaɗo da dangantakar al’adu, tarihi da diflomasiyya tsakanin Afirka da yankin Caribbean.

Tinubu yana ziyarar ƙasashen Caribbean da Kudancin Amurka a matsayin wani ɓangare na wata muhimmiya tafiyar diflomasiyya wanda ya zama ɗaya daga cikin shugabannin Afirka kaɗan da suka samu irin wannan lambar yabo ta musamman.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata