Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta kawo ƙarshen hare-haren da suka addabi jihar Benue.
Gidan talabijin na Channels ya ambato sanarwar da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar na bayyana cewa umarnin ya biyo bayan harin da ya yi sanadin mutuwar mutum 59 a Yelewata, wanda ake zargin wasu makiyaya daga jihar Nasarawa ne suka kai.
Tinubu ya bukaci jami’an tsaro su tabbatar da dawowar zaman lafiya a yankin, yayin da Gwamnan jihar, Hyacinth Alia, ya ce alkaluman sun fito ne daga rahoton hukumomin tsaro.
