Tuesday, April 7, 2026
HomeUncategorizedTinubu ya ware wa bangaren tsaro kaso mai tsoka a kasafin kudin...

Tinubu ya ware wa bangaren tsaro kaso mai tsoka a kasafin kudin 2024

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya ware kaso mai tsoka a daftarin kasafin kudin shekarar badi, 2024.
A Larabar makon nan dai ne shugaban kasar ya gabatar da kasafin kudin Naira Tiriliyan 27.5 a gaban Majalisar dokokin kasar.
Bangaren tsaro dai na da Naira Tiriliyan 3.25, kusan kaso 12% na daukacin kasafin kudin.
Daga tsaro, sai bangaren ilmi da aka ware wa Naira Tiriliyan 2.2, kusan kaso 9%. Sai kuma bangaren kiwon lafiya mai Naira Tiriliyan 1.4.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata