Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuTinubu ya yi tir da hari kan matafiya a Filato

Tinubu ya yi tir da hari kan matafiya a Filato

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi tir da hari kan matafiya a Filato, tare da bai wa hukumomin tsaro umarnin gaggauta kamo duk masu hannu a laifin da ya kira tsantsar rashin imani.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya ce wajibi ne a kamo tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin don fuskantar hukunci.

Ya kuma bayyana lamarin a matsayin wani abu da ba za a laminta ba, inda ya bukaci gwamnatin ta Filato ta yi aiki da hukumomin tsaro don kawo karshen tashe tashen hankulan da ke faruwa a jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata