Jam’iyyar APC ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai ɓace ba, kuma bai ki halartar aikinsa ba, duk da maganganun da dan takarar shugaban kasa na Labour Party a 2023, Peter Obi, ya yi kan rashinsa bayyanar shugaban a idon jama’a.
A wata sanarwa da mai magana da yawun APC na Legas, Seye Oladejo, ya fitar, jam’iyyar ta ce Tinubu yana ci gaba da gudanar da manyan al’amuran gwamnati – daga tsare-tsare, tsaro, harkokin diflomasiyya zuwa gyaran tattalin arziki.
Oladejo ya ce shugabanci ba a auna shi da fitowa kullum a kafafen watsa labarai ba, sai dai ingancin matakai da sakamakon ayyukan gwamnati.
A baya bayan nan, Peter Obi ya yi tambaya kan inda Tinubu ys shiga, yana cewa shugaban ya shafe kwanaki 196 a waje a 2025, kuma bai yi jawabi ga ‘yan kasa ba tun December 2025.
Tinubu dai ya isa Abu Dhabi domin halartar gangamin Abu Dhabi Sustainability Week 2026, bayan kammala hutun ƙarshen shekararsa a Turai.
