Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta kara harajin kashi 10% ga duk wata kasa da ke goyon bayan manufofin da ya kira na “adawa da Amurka” daga kungiyar kasashe masu tasowa ta BRICS.
Trump ya fadi hakan ne yayin da shugabannin kungiyar BRICS suka fara taron koli a birnin Rio de Janeiro, Brazil, ranar Lahadi.
Kungiyar BRICS, wadda ke dauke da kasashe irin su Brazil, Rasha, Indiya, China da Afrika ta Kudu, na kokarin zama madogara ta diflomasiyyar kasa da kasa, musamman a lokacin da kungiyar G7 da G20 ke fama da sabani da kuma rikicin manufofi da ya biyo bayan tsauraran matakan Trump na “America First.”
A cikin wata sanarwa da kungiyar BRICS ta fitar daga taron koli a Rio de Janeiro, ta nuna damuwa kan yadda karin haraji ke barazana ga cinikayyar duniya, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ambato.
