Thursday, April 9, 2026
HomeBabban LabarinmuBuhari na murmurewa a jinyar da yake yi a London - Garba...

Buhari na murmurewa a jinyar da yake yi a London – Garba Shehu

Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, mai shekara 82, na karɓar magani a birnin Landan tun daga watan Afrilu.

Buhari, wanda ya sauka daga mulki a 2023 bayan kammala wa’adin mulki na biyu, ya fara tafiya ne don duba lafiyarsa, amma daga bisani ya kamu da rashin lafiya tare da shafe kwanaki a dakin kulawa ta musamman (ICU).

DW Africa ta ruwaito mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya tabbatar da cewa Buhari na fama da rashin lafiya kuma yana jinya a Landan, amma bai bayyana asalin cutar ko asibitin da yake kwance ba.

Ana sa ran zai dawo gida Najeriya da zarar ya murmure.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata