DW Afrika ta ruwaito cewa bayan zaman tattaunawa tsakanin shugabannin ƙasashen biyu Recep Tayyip Erdogan da Hassan Sheikh Mohamud a birnin Istanbul, sun bayyana cewa wannan shi ne karon farko a tarihin Somaliya da za a fara hakar man fetur a tekun ƙasar.
Karkashin yarjejeniyar, Turkiyya za ta tura jirgin hakar mai zuwa tekun, kuma ana sa ran aikin zai taimaka a ɓangaren makamashi ga Somaliya, tare da yin tasiri ga tattalin arziƙin kasar.

Comment:Allah yarabaku da sharrin munafikan kasashen yamma.