Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaWadanda idanunsu suka rufe wajen son mulki ne kawai ke cewa a...

Wadanda idanunsu suka rufe wajen son mulki ne kawai ke cewa a tunbuke Shugaba Tinubu daga mulkin Nijeriya – Onanuga

Mai bai wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin yada labarai da dabarun siyasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa masu kira da a sauke shugaban kasa daga mulki ba komai ba ne face ‘yan siyasa masu kwaɗayin mulki.

Onanuga ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, inda ya mayar da martani kan hirar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi a tashar Channels Television a daren Lahadi.

Ya zargi El-Rufai da kasancewa a sahun gaba wajen neman sauke shugaban kasa, duk da cewa shi kansa ya taba bayyana cewa shekara hudu ba ta isa wani shugaba ya kawo gagarumin sauyi ba.

Onanuga ya yi ikirarin cewa gwamnatin Tinubu ta samu nasarori a cikin shekaru biyun da ta yi, ciki har da ƙaruwa kuɗaɗen shiga ga kasa da sauran abubuwan ci gaba.

RELATED ARTICLES

1 COMMENT

  1. Gaskiya Onanuga qarya kake, mu Talakawa zamu fada maka Halin qunci da muka shiga sakamakon Manufofin Gwamnatinku marasa amfani. Amma Insha’allahu daga 2027 TINUBU ya gama cin TALIYAR Qashe a VILA, ka rubuta ka aje

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata