DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeBabban LabarinmuKafa 'yan sandan jihohi a Nijeriya ba zai zama mafita ga tsaro...

Kafa ‘yan sandan jihohi a Nijeriya ba zai zama mafita ga tsaro ba – Hon. Gagdi

Dan majalisar tarayya mai wakiltar Pankshin/Kanke/Kanam a jihar Filato, Hon. Yusuf Gagdi, ya bayyana rashin goyon bayansa ga ƙoƙarin kafa ‘yan sandan jihohi a Nijeriya.

Gagdi ya yi wannan bayani ne a ranar Lahadi yayin ziyarar da ya kai wa al’ummomi da ke fama da matsalar tsaro a ƙaramar hukumar Kanam ta jihar Filato.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun ƙara mamaye yankunan Garga, Kukawa, Kyaram, Gyambau, Dungur da Shuwaka, lamarin da ya haifar da tsoro ga mazauna yankunan a jihar.

A cewarsa, kafa ‘yan sandan jihohi ba zai warware matsalar tsaro a Nijeriya ba, illa ma ya ƙara dagula lamura, domin gwamnoni na iya amfani da su wajen cin zarafin abokan hamayyarsu na siyasa.

Maimakon haka, ya ce kamata ya yi a ƙarfafa hukumomin tsaro na da kayan aiki, a ba ‘yan sanda, sojoji, DSS da sauran su isasshen kuɗi tare da tabbatar suna abin da ya dace.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata