Monday, April 6, 2026
HomeUncategorizedWani mutum ya kwanta dama bayan ya cinna musu wuta shi da...

Wani mutum ya kwanta dama bayan ya cinna musu wuta shi da matarsa a Jihar Ondo

Yan sandan Najeriya 

Rundunar yan sandan jihar Ondo ta tabbatar da mutuwar wani mutum da ba a bayyana sunansa ba, bayan da ya cinna musu wuta shi da matarsa, a yankin Ijoka ta ƙaramar hukumar Akure a Jihar.

A wata sanarwa da Rundunar yan sandan jihar ta wallafa a shafinta na X ranar Juma’a, ta ce ma’auratan sun shafe shekaru goma da yin aure kuma suna da yara biyu, kafin su rabu saboda wata matsala da ba a bayyana ba.

A cewar, yan sandan, mutumin ya dauki wannan danyen hukuncin ne bayan da matar taki amincewa su sasanta kan su, su ci gaba da rayuwa a matsayin ma’aurata.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata