Kotu a birnin Yamai ta saki hudu daga cikin ministocin gwamnatin hambararren shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum
Ministocin da aka sakin sun hada tsohon ministan makamashi malan Ibrahim Yacouba, sai tsohon ministan kudi Mohamed Djidoud, sai kuma tsohon ministan fasali Dr Rabiou Abdou sai a karshe tsohon ministan cikin gida Hama Adamou Souley.
Daman dai an kama wadannan ministoci ne da sauren wasu mukarabban tsohuwar gwamnatin ta hambararren shugaban kasar tun washe garin juyin mulkin sakamakon zargin su da furta kalaman cin amanar kasa da yi mata zagon kasa
A yanzu dai ko baya ga hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum, sauren manya manyan mukarabban nashi da ake cigaba da rike wa sun hada da tsohon ministan man fetur wato Mahaman Sani Mahadou da aka fi sani da suna Abba, da shugaban jam’iyyar PNDS Tarayya na kasa Malan Foumakoye Gado, akwai kuma tsohon dan majalisar dokoki kuma tsohon ministan tsaro a tsohuwar gwamnatin shugaba Issoufou Mahamadou wato malan Kalla Moutari da kuma tsohon ministan ilimi shi ma a lokacin gwamnatin Issoufo Daouda Mamadou Martai da sauran su.
Sakin wadannan tsoffin ministoci na hambararriyar gwamnatin ta Bazoum na zuwa ne kwanaki uku da cikar sojoji shekara guda akan karagar mulkin kasar.



