Rahotanni sun ce wata annoba ta bulla a wasu sansanonin ’yan bindiga a jihohin Neja da Zamfara, lamarin da ake cewa yana kara tsananta halin da suke ciki tare da shafar ayyukansu.
Majiyoyi sun bayyana wa jaridar Daily Trust cewa barkewar cutar na zuwa ne a daidai lokacin da suke fama da karancin abinci, kudade da magunguna, abin da ake zargin yana haifar da matsin lamba a cikin kungiyoyin tare da rage karfin aikinsu a wasu yankunan da abin ya shafa.
Wani mutum da ya tsere daga hannun masu garkuwa a Jihar Neja, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ya shaida yadda waɗanda ake tsare da su daga cikin ’yan bindigar ke fama da cututtuka daban-daban yayin da yake cikin sansanin.
