Wata ƙungiya a cikin jam’iyyar APC a jihar Bauchi ta bayyana rashin amincewarta da rahotannin da ke cewa gwamnan jihar, Bala Mohammed, na shirin ficewa daga PDP domin komawa APC.
Ƙungiyar mai suna APC Solidarity Group & Allied Associations ta bayyana matsayarta ne cikin wata sanarwa da jami’anta suka fitar a ranar Asabar.
Ƙungiyar ta ce har ma ta aika da takardar koke zuwa ga shugaban APC na ƙasa, inda ta lissafa dalilai guda goma da suka sa bai kamata a karɓi gwamnan cikin jam’iyyar ba yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027.
