Thursday, April 9, 2026
HomeBabban LabarinmuWike ya ce zai kyale Fubara ya yi gaban kansa a zaben...

Wike ya ce zai kyale Fubara ya yi gaban kansa a zaben kwamashinoninsa

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa ba shi da wani shiri na ba wa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, shawarar sunayen kwamishinoni a sabuwar gwamnatin sa.

Wike ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today da gidan talabijin na Channels ranar Alhamis, bayan dawo da gwamnatin Fubara daga dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya ayyana a jihar tsawon watanni shida.

A watan Maris ne aka ayyana dokar ta-ɓacin, bayan rikicin siyasa tsakanin Fubara da Wike ya kazanta, wanda da dama suka danganta shi da zargin cewa Wike yana tursasa wa Fubara nada mukarraban sa a gwamnati.

Sai dai Wike ya ce yanzu bai da wanda zai ba da shawarar sunansa, yana mai jaddada cewa zai bar wa gwamnan cikakken ikon gudanar da harkokin mulkin jihar mai arzikin mai a Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata