Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuWike ya musanta jita-jitar tsayawarsa takarar shugabancin Nijeriya a zaben 2027, ya...

Wike ya musanta jita-jitar tsayawarsa takarar shugabancin Nijeriya a zaben 2027, ya jaddada goyon bayansa ga Tinubu har zuwa 2031

Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya karyata rahotannin da ke cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP na matsa masa lamba domin ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaben 2027.

A wata sanarwa da mai taimaka masa kan hulɗa da jama’a da kafafen sadarwa, Lere Olayinka, ya fitar a ranar Asabar, ya bayyana labarin da wata kafar labarai ta wallafa a intanet a matsayin ƙarya daga mutanen da ba su da abin yi face ɓata suna.

Olayinka ya ce wannan rahoton yunƙuri ne na jawo Wike cikin ce-ce-ku-ce marar tushe, ya kuma jaddada cewa a wajen Wike Bola Tinubu ne kadai har zuwa 2031 Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A cewarsa, Wike mutum ne mai faɗin gaskiya ba ya da nuku-nuku, waɗanda ke son su ɓata masa suna sun rasa abin faɗa ne kawai.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata