Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuWike ya soke lasisin iznin mallakar filayen Ganduje, Sule Lamido, Patience Jonathan,...

Wike ya soke lasisin iznin mallakar filayen Ganduje, Sule Lamido, Patience Jonathan, Iyabo Obasanjo da karin wasu mutane

Fitattun sunayen da jaridar PREMIUM TIMES ta gani a jerin waɗanda Ministan na Abuja Nyesom Wike ya soke lasiain mallakar filayen na su, sun haɗa da Uwargidan tsohon Shugaban Nijeriya, Patience Jonathan, tsohon Ministan Tsaro, Theophilus Danjuma, tsohon babban Sojojin Ƙasa na Nijeriya, Ishaya Bamaiyi, da Iyabo Obasanjo, ‘yar tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo.

Sauran sunayen sun haɗa da; Sarkin Ilorin Ibrahim Sulu-Gambari; tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa, Uche Secondus, da tsohon mukaddashin shugaban jam’iyyar, Abubakar Baraje.

Tsofaffin gwamnoni da aka soke musu takardun mallakar ƙasa sun haɗa da Abdullahi Ganduje (Kano), Sule Lamido (Jigawa), Ayo Fayose (Ekiti), Olagunsoye Oyinlola (Osun), Donald Duke (Cross River), Niyi Adebayo (Ekiti), Ibrahim Dankwambo (Gombe) da Aliyu Wamakko (Sokoto).
Tsofaffin ministocin da ke cikin jerin sun haɗa da Kema Chikwe, Dapo Sarumi, Idika Kalu, Olu Agunloye, da Inna Ciroma.

‘Yan majalisa masu ci da wadanda suka taba zama ‘yan majalisa da sunayensu ke cikin jerin sun haɗa da Ali Ndume (Borno), Osita Izunaso (Imo), Caleb Zagi (Kaduna), Ganiyu Solomon (Lagos), Olabode Olajumoke (Ondo), Iya Abubakar (Adamawa), Abubakar Sodangi (Nasarawa), Iyiola Omisore (Osun), Patrick Obahiagbon (Edo), Usman Bugaje (Katsina), Abba Aji (Borno), Shehu Agaie (Niger), Patience Ogodo (Ebonyi), da Mao Ohuabunwa (Abia), wanda shi ne shugaban kwamitin amintattu na ɓangaren PDP na Wike.

Fitattun ‘yan Nijeriya da suka rasu amma sunayensu ke cikin jerin sun haɗa da ɗan takarar shugaban ƙasa na NRC a 1993, Bashir Tofa, tsohon shugaban BoT na PDP kuma minista, Tony Anenih, tsohon Ministan Kuɗi, Adamu Ciroma; tsohon jagoran Ohanaeze, Emmanuel Iwuanyanwu; wani tsohon shugaban Ohanaeze, Ralph Uwechue; tsoffin ministoci Alex Akinyele, Dubem Onyia, Onaolapo Soleye, Yakubu Lame, Babatunde Osotimehin, da John Odey.

Tsohon gwamnan Anambra Chinwoke Mbadinuju, tsohon IGP Ibrahim Coomassie, da Sanatan Delta North Patrick Osakwe, su ma sun rasu amma sunayensu na cikin jerin.

Hukumomin gwamnatin tarayya da lamarin ya shafa sun haɗa da Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (ONSA), NNPCL, ma’aikatun tarayya na Kuɗi, Muhalli, CBN, NTA, NPA, FHA, RMFAC, NAN; Rundunar Sojan Ruwa da Rundunar ‘Yan Sanda ta Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata