Sunday, April 5, 2026
HomeUncategorizedYadda cibiyar Nana Khadija ke taimakon wadanda aka ci zarafin su a...

Yadda cibiyar Nana Khadija ke taimakon wadanda aka ci zarafin su a Sokoto

Cin zarafin mata da yara yana daga cikin manyan matsalolin da ke ci gaba da barazana ga lafiyar jama’a da mutuncin al’umma. Duk da haka, yawanci waɗanda abin ya shafa ba sa kai rahoto saboda tsoro, kunya, da al’adun da ke hana magana.

A Sokoto, wannan matsala ta dade tana ɓoye ne a cikin shiru — har sai da aka kafa Cibiyar Nana Khadija Sexual Assault Referral Centre (SARC), wadda ta tashi tsaye wajen tallafa wa mata da yara da aka ci zarafinsu ta hanyar ba da kulawa, shawara, da taimakon da suke bukata.

A cewar rahoton ƙungiyar Invictus Africa, an samu rahotanni 1,762 na cin zarafi a Sokoto a shekarar 2023. Wannan adadi ya nuna irin yawaitar matsalar da ake fama da ita a cikin al’umma.

Alhaji Sani Umar Jabbi Sarkin Yakin Gagi, wani shugaban al’umma ne a jihar Sokoto, ya bayyana cewa, rashin ilimi da rashin dokoki ko hukunta wadanda suka aikata laifin cin zarafi, na daga cikin abubuwan da ke kara haddasa wannan matsalar.

Sarkin Yakin Gagi, Sokoto.

“A baya idan an sami mace ko yaro da aka yi wa fyade, iyalai kan yi shiru saboda suna tsoron abin kunya ko zargi. Wannan shiru shi ke sa mutane su ƙara shiga cikin raɗaɗi.”

Sai dai a yanzu, Cibiyar Nana Khadija wacce aka kafa a shekarar 2020 ƙarƙashin haɗin gwiwar Tarayyar Turai da Majalisar Ɗinkin Duniya (EU–UN Spotlight Initiative) tare da Gwamnatin Jihar Sokoto, ta zama mafaka ga waɗanda abin ya shafa.

Koodinetan cibiyar, Dokta Auwal Ahmad, ya ce suna karɓar mutanen da suka fuskanci cin zarafi cikin sirri da mutunci.

Dr Auwal Ahmed Musa

“Muna ba su taimako domin tabbatar da lafiyarsu, muna basu shawara don kwantar da hankalinsu, sannan muna tura su zuwa wani wurin idan matsalar ta fi karfinmu,” in ji Dokta Auwal.

A cewarsa, cibiyar tana tallafa wa mutum akalla 25 a kowane wata, adadin da ya nuna cewa yanzu mutane sun fara fita daga tsoron neman taimako.

Shugabannin al’umma sun tabbatar da cewa aikin cibiyar na sauya yadda mutane ke kallon batun cin zarafi.

“Yanzu mutane sun fara magana. Iyayen mata suna kai rahoto kai tsaye idan wani abu ya faru, kuma malamai suna faɗakar da jama’a cewa kare yara da mata wajibi ne. Wannan babban sauyi ne a al’umma,” in ji Sarkin Yakin Gagi.

Yayin da duniya ke gudanar da kwanaki 16 na yaƙi da cin zarafin mata da yara, cibiyar Nana Khadija ta zama alamar yadda haɗin gwiwar likitoci, malamai, da shugabannin al’umma ke samar haifar da mafita ga masu rauni a cikin al’umma.

Za ku iya kallon cikakken rahoton a nan: https://www.facebook.com/share/v/19n1XGyyth/

Wannan labari ya zo muku ne da tallafin kungiyar Nigeria Health Watch a wani ɓangare na shirin yaɗa labarun samar da sauyi a Afirka

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata