Monday, April 6, 2026
HomeUncategorized'Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu dalibai mata 4 a jihar...

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu dalibai mata 4 a jihar Benue

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Benue ta tabbatar da sace dalibai mata 4 na jami’ar aikin gona ta gwamnatin tarayya da ke Makurdi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Benue, CSP Sewuese Anene, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho da gidan talabijin na Channels, inda ya ce an fara gudanar da bincike tare da nemo inda suke.

Wasu majiyoyi a kusa da jami’ar sun ce wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da daliban ne a harabar jami’ar da misalin karfe 8:30 na dare, lamarin da ya haifar da firgici ga daliban.

Yace daliban da aka yi garkuwa da su sun hada da, Emmanuella Oraka, Fola, Susan da kuma Ella.

A halin da ake ciki dai labarin sace daliban ya haifar da zanga-zanga daga daliban da suka zagaye makarantar inda suka bukaci mahukuntan makarantar su dauki matakin gaggawa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata