Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasa'Yan majalisar dokokin Nijeriya 53 ne suka yi zaman dumama kujera tsawon...

‘Yan majalisar dokokin Nijeriya 53 ne suka yi zaman dumama kujera tsawon shekara daya ba su ba da gudunmuwa a majalisa ba

Aƙalla mambobin Majalisar Wakilai 48 da Sanatoci 5 sun kasa shiga wata muhawara, daukar nauyin kudurori ko gabatar da koke-koke a majalisar dokoki cikin tsawon watanni 12, a cewar wani sabon rahoto da aka fitar a ƙarshen mako.

Rahoton ya fito ne daga Deliberative Barometer and Policy-Focus Productivity Report (NASS-DBPFR), wanda Erudite Growth and Advancement Foundation (ERGAF-Africa) ta wallafa, inda aka bibiyi ayyukan majalisa daga ranar 14 ga Yuni, 2023 zuwa 13 ga Yuni, 2024.

A cewar rahoton, waɗannan ‘yan majalisar ba su yi ko da ɗaya daga cikin ayyukan zaman majalisa ba a lokacin da aka duba. An jaddada cewa gazawarsu na shiga muhawarar majalisa ko daukar nauyin kudurori na rage ingancin doka da kuma saɓa tsarin mulkin dimokuraɗiyya.

RELATED ARTICLES

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata