DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, April 13, 2026
HomeLabarai’Yan majalisar wakilai na ADC sun bukaci a cire shugaban INEC

’Yan majalisar wakilai na ADC sun bukaci a cire shugaban INEC

’Yan majalisar wakilai na ADC sun bukaci a gurfanar tare da cire shugaban INEC, Joash Amupitan, bisa zargin nuna bangaranci kafin zaben 2027.

Sun bayyana haka ne bayan taronsu na farko, inda suka ce zarge-zargen da ake yi wa shugaban hukumar, musamman batun wani asusun X da ake dangantawa da shi, na iya lalata amincewar jama’a da tsarin zabe, duk da cewa INEC ta musanta alakar sa da asusun.

’Yan majalisar sun kuma zargi hukumar da katsalandan a rikicin cikin gida na jam’iyyar, tare da gargadin cewa irin wadannan matakai na iya kawo cikas ga dimokuradiyya, suna mai kira ga a gudanar da bincike domin kare sahihancin zabe a Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata