DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
HomeBabban Labarinmu'Yan Najeriya ba za su sake zabar Tinubu ba - PDP

‘Yan Najeriya ba za su sake zabar Tinubu ba – PDP

Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce shugaba Bola Tinubu ya fara shirye-shiryen mika mata ragamar mulki domin kuwa ‘yan kasar ba za su sake zabar sa ba.

Yayin tattaunawa da jaridar Punch a sakatariyar jam’iyyar da ke Yola, sakataren tsare-tsaren PDP a jihar Adamawa Hamza Madagali, ya ce ‘yan Najeriya ba su da karfin sake jure irin shugabancin gwamnatin APC a 2027.

A cewar sa, tsare-tsaren da gwamnatin APC ke bullo da su ba su yi daidai da al’umma da kuma tattalin arzikin Najeriya ba.

Ya kara da cewa a halin yanzu’ yan Najeriya sun kara wayo, saboda haka ba za su yadda su salwantar da makomar ‘ya’yansu ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata