Sunday, April 5, 2026
HomeBabban Labarinmu‘Yan Nijeriya miliyan 83 ne ke fama da talauci, kashi 10 ne...

‘Yan Nijeriya miliyan 83 ne ke fama da talauci, kashi 10 ne kawai ke riƙe da kashi 90 na dukiyar Nijeriya – Oxfam

Daraktan ƙungiyar Oxfam a Nijeriya, John Makina, ya koka kan yadda rashin daidaito ke ƙara tabarbarewa a Nijeriya, yana mai cewa ana ci gaba da bai wa ‘yan kaɗan masu gata dama tare da sanya akasarin mutane cikin talauci.

Makina ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Alhamis a wajen wani taron tattaunawa kamar yadda jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito.

Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki daga majalisar dattawa, manyan ma’aikatu, ofisoshin jakadanci, ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, da ƙungiyoyin farar hula.

Da yake jawabi a wurin taron, Makina ya koka da cewa rashin daidaito ya bayyana a fili a yadda ake mayar da matasa saniyar ware a siyasance.

Ya ce a halin yanzu babu matashi wanda bai wuce shekara 35 ba a majalisar ministocin tarayyar Nijeriya.

“Gaskiyar magana ita ce, kashi 90 cikin 100 na albarkatun Nijeriya wasu ne ke da iko da su, kuma ‘yan ƙasar sama da miliyan 83 ne ke rayuwa a ƙasa da Naira 3,100 a rana” in ji Makina.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata