Monday, April 6, 2026
HomeBabban Labarinmu'Yan Nijeriya na sayen mai da sauki fiye da wasu ƙasashen Afrika...

‘Yan Nijeriya na sayen mai da sauki fiye da wasu ƙasashen Afrika – Dangote

Shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya na biyan kashi 55 ne kawai cikin 100 na abin da wasu a ƙasashe makwabta ke biya na man fetur.

A cikin wani sakon email da ya aike wa gidan Talabijin na Channels a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce Dangote ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da shugaban hukumar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, Dakta Omar Touray, da tawagarsa suka kai a matatarsa da ake tace ganga 650,000 a kowacce rana.

Ya jaddada cewa an samu raguwar farashin sakamakon tace man fetur a cikin gida, wanda ke ci gaba da inganta karfin man fetur tare da inganta tsaro da kuma rage dogaro da shigo da kayayyaki daga kasashen waje.

Da yake magantawa, Touray ya ayyana matatar man Dangote a matsayin abin alfahari ga Afirka, tare da bayyana ta matsayin abin koyi ga kamfanoni masu zaman kansu domin bunkasa masana’antu a yankin.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata