Wednesday, April 8, 2026
HomeBabban Labarinmu'Yan Nijeriya sun saba da samun kudin banza shi ya sa ba...

‘Yan Nijeriya sun saba da samun kudin banza shi ya sa ba su ganin kokarin da Shugaba Tinubu ke yi – Sanata Orji Kalu

Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana haka ne yayin da yake kare manufofin tattalin arzikin shugaban kasa Bola Tinubu, inda ya ce ‘yan Nijeriya na sukar manufofin Tinubu ne saboda sun saba samun kudin banza ba tare da yin aiki ba.

Da yake zantawa da manema labarai a zauren majalisar a ranar Talata, 27 ga watan Mayu, 2025, tsohon gwamnan jihar Abia, ya amince da wahalhalun da kasar nan ke ciki a halin yanzu, amma ya bukaci ‘yan kasar da su yi hakuri, yana mai cewa alfanun da ke tattare da sauye-sauyen tattalin arzikin da ake yi zai bayyana a shekaru masu zuwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata