Monday, April 6, 2026
HomeUncategorized'Yan sanda a Adamawa sun kama wasu jami'an hukumar bada agajin gaggawa...

‘Yan sanda a Adamawa sun kama wasu jami’an hukumar bada agajin gaggawa tare da wasu ‘yan banga bisa zargin zamba

‘Yan sanda a Adamawa sun kama wasu jami’an hukumar bada agajin gaggawa tare da wasu ‘yan banga bisa zargin zamba

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta dakile wani shiri na aikata zamba tsakanin ma’aikatan hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Adamawa (ADSEMA) da ‘yan banga ke shirin yi.

A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya fitar, yace rundunar ta samu bayanai game da shirin da ake shirin da wayan da ake zargin suka yi, inda nan take ta tura wata tawaga zuwa rumbun ajiyar kayayyaki dake unguwar Limawa a karamar hukumar Yola ta Arewa.

Rundunar ‘yan sandan ta cafke mutane takwas da suka hada da ma’aikatan ADSEMA uku da ‘yan banga biyar, sannan ta kwato buhunan masara, gero, da masara 98.

Kwamishinan ‘yan sanda, CP Dankombo Morris, ya yabawa DPO Jimeta da tawagarsa bisa gaggaucewa da suka yi da kuma nuna kwarewa, wanda ya kai ga kamawa tare da kwato hatsin da aka sace.

Ya bukaci jama’a da su bayar da bayanai kan maboyar batagari ya kuma baiwa al’ummar jihar Adamawa tabbacin ‘yan sanda zasu ci gaba da kokarin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata