Tuesday, April 7, 2026
HomeUncategorized‘Yan sanda sun kama wasu masu garkuwa da mutane a Katsina

‘Yan sanda sun kama wasu masu garkuwa da mutane a Katsina

Police

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wasu mutane 8 da ake zargi da hannu wajen garkuwa da mutane, fashi da makami, da hada baki wajen kisan kai da sauran laifuka a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abubakar Sadiq, shine ya gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Laraba.

Ya ce rundunar ta kama wani matashi dan shekara 16, Nuhu Haruna da ke kauyen Fenza, a karamar hukumar Dutsinma da alaka da wanda ake zargi da aikata laifin kisan kai.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma kama wani Abubakar Nasiru mai suna Haro da ake zargi da laifin hada baki da kuma garkuwa da mutane.A ci gaba da gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa laifin aikata laifin, sannan ya kara da cewa ya karbi kudi naira miliyan biyu a matsayin kason sa na kudaden da aka samu na garkuwa da mutane.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata