Monday, April 6, 2026
HomeBabban Labarinmu'Yan sandan jihar Katsina sun musanta labarin barayin daji sun karbe ikon...

‘Yan sandan jihar Katsina sun musanta labarin barayin daji sun karbe ikon karamar hukumar Kankara ta jihar

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce tana sane da wani labari da ta kira na karya da ake yadawa musamman a kafar sadarwar X cewa barayin daji sun karbe ikon yankin karamar hukumar Kankara ta jihar.

A cikin sanarwar da kakakin rundunar DSP Sadiq Abubakar Aliyu ya fitar, rundunar ‘yan sandan ta ce kwata-kwata babu kanshin gaskiya a labarin, an kirkiro shi ne kawai don a jefa tsoro a zukatan jama’a musamman na yankin karamar hukumar Kankara da sauran ‘yan jihar Katsina.

Rundunar ‘yan sandan ta bukaci mutane da su yi watsi da wadannan bayanai da ta kira na karya da ke yawo l. Sannan ta ba da tabbacin cewa tana nan tana bincike don zakulo waɗanda suka kitsa labarin don daukar matakin da ya dace a kansu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata