Rundunar ƴansandan jihar Zamfara ta bayyana samun nasarar dakile wani yunkuri daga ‘yan bindiga na tare wata babbar hanya.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar na jihar DSP Yazid Abubakar ya fitar, ta bayyana cewa a ranar 21 ga watan Disamban 2025, jami’an sashen hana garkuwa da mutane na rundunar karkashin jagorancin ASP Aliyu Bilyaminu Koko, ta samu bayanan sirri kan cewa ‘yan bindigar sun tare hanyar Tsafe zuwa Yanwarin Daji.
Hakan ya sa suka kai dauki wajen, inda suka yi artabu da ‘yan ta’addan, lamarin da yayi sanadiyyar jikkatar wasu da dama da suka tsere, aka kuma kama mutum guda mai suna Umar Alhaji Bukar da aka fi sani da Bingil wanda ya mika wuya.
Rundunar ta jinjinawa jami’an tare da al’umma wadanda suka taimaka wajen bayar da bayanan sirrin kan yunkurin ‘yan bindigar.
