Tuesday, April 7, 2026
HomeBabban LabarinmuShugaban Saliyo ya fara aiki a matsayin shugaban ECOWAS

Shugaban Saliyo ya fara aiki a matsayin shugaban ECOWAS

Leone Julius Maada Bio, Shugaban kasar Sierra, wanda shi ne zababben shugaban kungiyar ta ECOWAS, ya yi alkawarin mayar da hankali wajen maido da tsarin mulki da zurfafa dimokaradiyya a yankin kasashen yammacin Afirka.

Ya karbi ragamar shugabancin ECOWAS daga hannun shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya a ranar Lahadi a Abuja, a taron hukumar karo na 67, da ya gudana.

Tinubu ya yi wa’adi biyu ne a matsayin shugaban kungiyar ta ECOWAS.

A jawabinsa bayan karbar ragamar, shugaba Bio ya yi alkawarin jagorantar sabuwar kungiyar ECOWAS mai kishin jama’a da kuma aiwatar da ayyukan ci gaba a daidai lokacin da ake fuskantar kalubale da damammakin da ba a taba gani ba a yankin yammacin Afirka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata