Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuYanzu Najeriya na da ƙarfin hako ganga miliyan 2 na man fetur...

Yanzu Najeriya na da ƙarfin hako ganga miliyan 2 na man fetur a rana – NUPRC

Hukumar kula da harkokin man fetur ta Nijeriya (NUPRC) ta bayyana cewa yanzu haka Najeriya na da ƙarfin samar da ganga miliyan 2 na man fetur a kowace rana.

Sai dai hakan ya yi ƙasa da burin gwamnati na fitar da ganga miliyan 2.2 a kowace rana kamar yadda aka tsara a kasafin kudin shekarar 2025.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar jiya Laraba, ta ce Najeriya na kan hanyar cika adadin da OPEC ta ware mata, sakamakon wasu matakai da aka ɗauka tare da haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki a masana’antar domin ƙara yawan adadin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata