Musulmin duniya na cike da burin ziyarar dakin Ka’aba don sauke farali wato aikin hajji, da ke zaman daya daga cikin rukunan Musulunci
Akwai wuraren da alhazan da suka je aiki ke ziyarta da masana suka kiyasta nisan tafiyar ta fuskar yawan kilmitoci da mintinan da mahajjata ke kwashewa a yayin aikin hajji.
Ga jadawalin yadda nisan wuraren da ake zuwa ziyarori yake a yayin aikin hajjin kowace shekara a kasar Saudiyya;
Aranar 8 ga watan zulhijja ne ranar da alhazai gaba daya zasu fita daga masaukinsu suyi harama kan aikin hajji inda zasu tafi Mina/Muna kuma zasu kwana achen bayan wayer gari ne zasu wuce filin arafat wanda yakama kilometre 14
Daga filin Arafat zuwa muzdalifa kuma nada tsawon kilometre 8, daga nan kuma sai zuwa jamarat wanda daga munzalifa zuwa jamarat ake tafiyar kilometre 4
Toh daga jamarat ne kuma sai tafiya Masjid alharam wanda daga jamarat zuwa Masjid alharam ake tafiyar kilometer 5
Kadan kenan daga cikin kilmitocin da mahajjata ke sharewa a yayin aikin hajji a kasar Saudiyya.
Sau nawa ku ka taba zuwa aikin hajji?
