Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuYawancin ma su rawar kafar kawar da Tinubu ba domin jin ƙan...

Yawancin ma su rawar kafar kawar da Tinubu ba domin jin ƙan jama’a suke ba – Shehu Sani

Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya kuma mai rajin kare hakkin dan Adam, Shehu Sani, ya ce yawancin ma su sukar takun gwamnatin Tinubu ba domin jin ƙan jama’a suke ba, sai don fushin an hana su mukami da gaza cimma muradun siyasa.

A wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Channels, ya ce yawancin ’yan adawan suna daga cikin tsaffin masu mulki ne tun 1999 da suka rasa matsayi yanzu.

Ya ƙara da cewa babu bambanci a tsakanin su da masu mulki, dukkansu daga ƙungiyar ’yan siyasar elite su ka fito.

Shehu Sani ya kuma ce bai dace a dora wa Tinubu laifin rikicin da ke cikin jam’iyyun adawa ba, inda ya soki yunƙurin kafa kawance na siyasa da Atiku da sauran manyan ’yan siyasa ke yi don 2027.

RELATED ARTICLES

4 COMMENTS

  1. To, na yarda da maganar comrade. Amma ina so in tambaye shi, shi yana ganin cewa, Tinubu ya cancanta ya cigaba da mulki bisa tamarin tsarin salon mulkin sa? Kuma shi mulkin na shugaba Tinubu a hangen comrade Sani, yana tausaya wa jama’a, musamman talaKawa?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata