DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeLabaraiZa a dakatar da daliban da ke tsangwamar abokan karatunsu - Gwamnatin...

Za a dakatar da daliban da ke tsangwamar abokan karatunsu – Gwamnatin Nijeriya

Ma’aikatar ilimi ta tarayya ta yi gargadin cewa duk dalibin da aka samu da laifin cin zarafin da ya kai ga taba lafiyar abokan karatunsu, za a dakatar da shi daga kwalejojin tarayya har sai yadda hali yayi.
Wata takardar umurni da babban sakataren ma’aikatar, Nasir Gwarzo, ya sanyawa hannu ta ce ba za su zuba ido dalibai na raunata junansu ba a cikin makarantu.
Sanarwar ta ce ko a ranar 7 ga watan Nuwamba, gwamnatin tarayya ta bada umurnin dakatar da wasu dalibai 13 na tsawon makonni 6 a jihar Enugu har sai an gudanar da bincike kan zargin da ake musu na tsangwamar abokan karatunsu.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata