Gwamnatin Nijeriya tare da kungiyar ActionAid Nigeria, sun bayyana aniyarsu ta kawar da talauci a Nijeriya kafin shekarar 2030 ta hanyar aiwatar da tsare-tsare waɗanda za su ƙarfafa wa mutane da ba da dama ga masu aiki tukuru.
Daraktan kungiyar ActionAid Nigeria, Andrew Mamedu, ya ce kawar da talauci zai yiwu ne idan gwamnati da ‘yan ƙasa suka haɗa kai tare da bin hanyoyi masu kyau da fadada Tunani.
Ya nuna damuwa kan yadda kasafin kuɗin Nijeriya ya ƙaru daga Naira biliyan 300 a 1999 zuwa Naira tiriliyan 54.5 a 2024, amma talauci bai ragu yadda ake tsammani ba.
A cewarsa Nijeriya tana asarar kusan dala biliyan 18 a kowace shekara saboda kashe kudi ba bisa ka’ida ba.
Ya yi kira ga gwamnati ta koyi darasi daga ƙasashen China da India waɗanda suka fitar da miliyoyin mutane daga talauci ta hanyar saka jari a fannonin ilimi, lafiya, samar da ababen more rayuwa, da karawa marasa galihu karfi.
