DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
HomeUncategorizedZa a yi addu'o'i na musamman domin cikar Shugaba Tinubu shekaru 73...

Za a yi addu’o’i na musamman domin cikar Shugaba Tinubu shekaru 73 da haihuwa

Bola Ahmad 
A ranar Asabar ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, zai cika shekaru 73 a duniya, zai hadu da ‘yan uwa musulmi a babban masallacin kasa da ke Abuja domin gudanar da addu’o’i na musamman ga kasar.
 
Bikin zagayowar ranar haihuwar Shugaba Tinubu dai ta zo ne daidai lokacin azumin Ramadan kuma ta zo ne watanni biyu kafin cikar gwamnatinsa shekaru biyu.
A cikin wata sanarwa da mai bai wa Shugaban kasa shawara na musamman Bayo Onanuga ya fitar ta ce ana gayyatar al’umma domin yin addu’a ga kasa baki daya da kuma dorewar zaman lafiya a kasar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata