Kakakin majalisar wakilai Tajuddeen Abbas ya nuna damuwa da yawan ciyo basuka da ake yi a Najeriya, yana mai bayyana hakan a matsayin lamarin da ke zama barazana ga dorewar tattalin arzikin kasar.
Da yake jawabi a ranar Litinin, yayin bude taron shekara na kwamitocin kula da asusun al’umma na Afirka ta yamma a Abuja, kakakin ya ce akwai bukatar sake yin duba kan tsare-tsaren ciyo bashin cikin gaggawa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Abbas na cewa tulin bashi a mafiya yawan kasashen Afirka, na hana gwamnatoci gudanar da muhimman ayyuka a sauran bangarorin da al’umma ke bukata irin su kiwon lafiya da dai sauran su.
