Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuZa mu yi sabuwar jam'iyya ne saboda gwamnatin APC ta gurbata jam’iyyun...

Za mu yi sabuwar jam’iyya ne saboda gwamnatin APC ta gurbata jam’iyyun adawa – Nasir El-Rufa’i

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa jiga-jigan ‘yan adawa na son fitowa da sabuwar jam’iyyar ne gabanin zaben 2027, saboda kutsen da ‘yan koren gwamnatin APC suka yi a cikin jam’iyyun da ake da su a yanzu.

Ya ba da misali da rikicin cikin gida dake faruwa a jam’iyyun PDP da LP da kuma NNPP.

A wata hira da gidan talabijin na Arise TV, El-Rufai ya ce bukatar yin rajistar jam’iyyar ADA da suka mika ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC wata dabara ce ta tsaftace hadakar daga duk wani kutse don kalubalantar shugaba Bola Tinubu a zaben dake tafe.

Sai dai El-Rufai ya zargi gwamnatin APC wajen kawo cikas ga yunkurin yin rijistar jam’iyyar ‘yan adawa.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata