Babban baturen zaben Sa’adu ya ce adadin masu kada kuri’a da aka yi wa rajista a rumfunan zabe da abin ya shafa ya kai 5,446, yayin da aka karbi katin zabe 3,265 a wuraren.
Ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta samu kuri’u 7,001, yayin da jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 5,339, abin da ya bar tazarar kuri’u 1,662.
Zaben ya gudana ne a mazabar Kaura Namoda ta Kudu a majalisar dokokin jihar Zamfara.
