Sanata Ireti Kingibe ta bayyana cewa zaben kananan hukumomi da ke tafe a babban birnin tarayya zai zama wani filin gwaji da zai bayyana yadda jama’a ke kallon Ministan Abuja, Nyesom Wike.
A wata hira da aka yi da ita a shirin Political Paradigm na Channels Television, Sanatar mai wakiltar Birnin Abuja ta ce, yawancin mazauna Abuja ba su gamsu da irin jagorancin da Ministan ba, kuma suna jin an ware su daga tsarin mulki da gudanarwa.
Sanata Kingibe ta kara da cewa Wike bai fahimci bukatun jama’ar Abuja ba, kuma bai mayar da hankali kan matsalolinsu, musamman na tsaro da gine-ginen ababen more rayuwa.

Of cost wike a you listinen you can change