DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
HomeBabban LabarinmuZan iya ajiye takara in mara wa matashi baya a 2027 -...

Zan iya ajiye takara in mara wa matashi baya a 2027 – Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa idan bukata ta taso, zai iya hakura da burinsa na neman shugabancin kasa a zaben 2027, domin bai wa wani matashi dama.

Atiku, wanda ke cikin manyan jagororin jam’iyyar ADC, ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da kafar yada labarai ta BBC Hausa ranar Laraba.

Ya ce idan wani matashi ya kayar da shi a zaben fidda gwani, zai mika wuya ya kuma goya masa baya da karfinsa da shawarwari.

Ya bayyana cewa babban burinsa a yanzu shi ne ƙarfafa haɗin kan jam’iyyar ADC, wacce a cewarsa ke ba da fifiko ga matasa da mata domin sanyasu a gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata