DCL Hausa Radio
Kaitsaye

A janye dakatarwar da aka yi ma Natasha ko kuma mu makaka kotu- SERAP ga Akpabio

-

Kungiyar SERAP mai fafutikar yaƙi da cin hanci a Nijeriya ta yi kira da babbar murya ga shugaban majalisar dattawan Nijeriya Godswill Akpabio da ya gaggauta janye dakatarwar da majalissa ta yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Kungiyar ta bayyana matakin dakatarwar a matsayin rashin bin doka da kuma take ma mata ‘yancin fadar albarkacin baki.

Wannan dai na a cikin wata budaddiyar wasika mai dauke da kwanan wata na 8 ga watan Maris 2025, wanda mataimakin daraktan kungiyar ta SERAP, Kolawole Oluwadare ya sa ma hannu, SERAP ta yi gargadin cewa za ta yi shari’a idan har shugaban majalisar dattawa ya ki bin gargadin cikin sa’o’i 48.

Leave a Reply to Anonymous Cancel reply

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Rukunin farko na maniyyatan jihar Bauchi a Nijeriya, sun tashi zuwa Saudiyya- NAHCON

Hukumar aikin Hajji ta Nijeriya ta bayyana cewa maniyyata 2,520 ne daga cikin jihar Bauchi za su halarci aikin Hajjin bana na 2025 a kasar...

An saki ‘Yan jaridar Sahara FM da aka tsare a Agadez

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na nuna cewa an saki ‘yan jarida uku na gidan rediyon Sahara FM da ke Agadez bayan da aka tsare su...

Mafi Shahara