Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa sabuwar kawancen jam’iyyu adawa na da karfin da zai kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027, ko da ba tare da goyon bayan gwamnoni ba.
El-Rufai, wanda kwanan nan ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar SDP, ya bayyana haka ne yayin wata hira da manema labarai a birnin Kano, inda ya ce dabarar da kawancen ke amfani da ita ita ce ta kai tsaye wajen tunkarar masu kada kuri’a, ba wai dogaro da masu rike da mukaman siyasa ba.
Wannan kalami na El-Rufai na zuwa ne a daidai lokacin da Kungiyar Gwamnonin PDP ta bayyana kin amincewa da kowacce irin hadaka ko kawance a kokarin yin maja da wasu jam’iyyun adawa ke yi kafin 2027.
Sai dai bayan taron da aka gudanar a Ibadan, karkashin jagorancin mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Ambasada Umar Damagum, da wasu gwamnoni, kungiyar ta nesanta kanta da wannan sabuwar tafiya, tana mai cewa jam’iyyar PDP za ta tsaya da kafafunta har zuwa 2027.