Hukumar Alhazai ta Nijeriya NAHCON ta ce an kwashe mahajjatan Nijeriya 1,622 zuwa Madina domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya rawaito cewa mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima kaddamar da fara jigilar jirgi na farko a garin Owerri na jihar Imo a ranar Juma’a.
Bayanan da babban jami’in watsa labarai na hukumar NAHCON, Shafii Mohammed ya fitar, ya bayyana cewa, Jiragen Alhazan Nijeriya guda uku da sun yi jigilar jirage hudu a jihohin Bauchi, Kebbi, Imo, da Legas.
Mohammed ya ce jiragen sun hada da MaxAir, Flynas, da Kuma Air Peace. A ranar Juma’a jirgin MaxAir mai lamba VM3001 ya tashi daga Bauchi zuwa Madina da karfe 11:53 tare da alhazan Bauchi 539 da jami’ai shida.