Jagoran cocin Katolika na duniya, Pope Leo XIV, ya yi kakkausar suka kan hare-haren soji da Amurka da Isra’ila ke kai wa Iran, yana mai gargadin cewa ba za a iya jingina yaƙi da addini ba, tare da jaddada cewa Ubangiji ba ya kaunar kowane irin zalinci.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana cewa mabiya Yesu-Almasihu, wanda ya kira Jagoran zaman lafiya, bai kamata su goyi bayan tashin hankali ba, yana mai cewa dole ne a maye gurbin yaƙi da tattaunawa da diflomasiyya domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa, yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ƙara tsananta.
