DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, April 14, 2026
HomeLabaraiAkpabio ya ce matsalar tsaron Nijeriya za ta zo karshe bayan zaben...

Akpabio ya ce matsalar tsaron Nijeriya za ta zo karshe bayan zaben 2027

Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio, ya danganta karuwar matsalar tsaro da ke addabar ƙasar da shirye-shiryen zaɓe mai zuwa, yana mai cewa bayan kammala zaɓen, lamarin zai ragu.

Akpabio ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin kaddamar da hedikwatar haraji ta Nijeriya NRS a Abuja, inda ya ce gwamnatin Bola Tinubu na yin aiki mai kyau, amma wasu ‘yan adawa suna ɗaukar nauyin rashin tsaro saboda sun rasa abin yi.

Ya ce, “Rashin tsaro yana ƙaruwa ne saboda zaɓe na zuwa. Mutane sun rasa abin yi, sai suka koma ɗaukar nauyin rikice-rikice. Amm bayan zaɓe, komai zai lafa.”

Haka kuma ya yi suka ga ‘yan adawa, musamman Peter Obi, inda ya ce akwai rikice-rikice a cikinsu, yana mai zargin cewa wasu daga cikinsu sun bar jam’iyyunsu duk da samun kuri’u masu yawa a zaɓen baya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Akpabio ya kuma roƙi ‘yan Nijeriya su ci gaba da haƙuri da gwamnatin Tinubu, yana mai cewa tana kan hanya madaidaiciya wajen gyara tattalin arziki da inganta rayuwar jama’a.

A wajen taron, ya yabawa shugaban hukumar haraji, Zacch Adedeji, inda ya ce shi ne ɗaya daga cikin masu karɓar haraji da jama’a ke so, sabanin yadda aka saba kallon ma’aikatan haraji a baya.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibrin, da Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, tare da wasu gwamnoni da manyan jami’an tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata